KWATANTA AUREN HAUSAWA NA GARGAJIYA DANA HUKUMAR HISBA A JIHAR KANO

Student: Amina Muhammad Musa
Supervisor: Prof Aliyu Mu'azu Zariya
HOD: Dr Yusuf Ahmad Gwaro
Department of Hausa
Humanities
Northwest University, Kano, Kano State

Abstract

TAƘAITACCEN BAYANI (ABSTRACT) Wannan bincike mai taken "Kwatanta Auren Hausawa na Gargajiya da na Hukumar Hisba a Jihar Kano" ya yi ƙoƙarin fito da bambance-bambance da kamance tsakanin auren gargajiya na Hausawa da auren da Hukumar Hisba ta Jihar Kano ke gudanarwa, musamman auren zawarawa ko auren marasa galihu (wanda aka fi sani da auren 'yan gata). An gudanar da binciken ne ta hanyar amfani da tsarin bincike na siffantawa (descriptive research), inda aka tattara bayanai ta hanyar tattaunawa da jami'an Hukumar Hisba, ma'auratan da suka amfana da shirin, da kuma ziyartar ɗakunan karatu domin duba littattafai da kundayen bincike masu alaƙa. An zaɓi samfurin bincike ne ta hanyar zaben kai tsaye (random sampling) daga cikin waɗanda suka shiga cikin shirin auren na Hukumar Hisba a shekarun 2012, 2014, 2015, da kuma na 2023. Sakamakon bincike ya nuna cewa auren Hukumar Hisba ya sha bamban da auren gargajiya ta fuskoki da dama. Auren gargajiya iyaye ne ke ɗaukar nauyi tare da bin matakai kamar toshi, lefe, baiko, da sa-rana, yayin da auren Hisba gwamnati ce ke shiryawa tare da samar da kayan aure, sadaki, walima, da kuma bitar wayar da kan ma'aurata kafin aure. Har ila yau, akwai ƙa'idojin hana saki ba tare da sanar da hukumar ba, da kuma bin diddigin zamantakewar ma'aurata bayan aure. Binciken ya kuma gano cewa dalilin kafa irin wannan auren shi ne domin magance matsalar yawaitar mutuwar aure, rashin halin da iyaye ke da shi na aurar da 'ya'yansu, da kuma rage yawan zawarawa da matasa marasa aure a cikin al'ummar Jihar Kano. Auren yana da tushe a cikin Alƙur'ani da Sunnah, kuma yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al'umma ta fuskar rage zina da fasadi da inganta zamantakewa. Daga ƙarshe, binciken ya ba da shawarar cewa gwamnati, attajirai, da malamai su ci gaba da tallafawa wannan shiri domin ya dore, kuma masu bincike na gaba su zurfafa nazari a kan tasirin wannan auren ga al'ummar Hausawa baki ɗaya. Keywords: Auren Hausawa, Auren Gargajiya, Hukumar Hisba, Auren Zawarawa, Auren Marasa Galihu, Jihar Kano

Full-Text Access Notice

In accordance with the NERD Policy on promoting peer-reviewed publication, public access to the full text of a project, thesis or dissertation is restricted for three years, allowing the author and supervisors sufficient time to pursue peer-reviewed publication. During this period, researchers with legitimate academic or research purposes may request authorisation directly from the author to enable NERD to release the indexed full texts of the work using the form below.

Request authorisation from the author