FASSARAR WANI ƁANGARE DAGA CIKIN LITTAFIN MUSANNAF IBN ABI SHAIBAH ZUWA HARSHEN HAUSA, DAGA HADISI MAI LAMBA TA 34500 ZUWA 34599
Abstract
TAƘAITACCEN TARIHIN IBN ABI SHAIBAH
MASHIGA
Wannan babi ya ƙunshi abubuwa kamar haka: Nasabar mawallafin da haihuwarsa da neman iliminsa da ƙarni ko zamanin da ya rayu, da kaɗan daga cikin Malamansa, da kaɗan daga cikin ɗalibansa, da waɗanda suka fitar da Hadisansa.
NASABARSA
Abubakar ɗan Muhammad ɗan Abu Shaibah ɗan Ibrahim ɗan Usman ɗan Kuwaiti ɗan Al'abasi, mutumin birnin Kufa, wanda a ke yiwa laƙabi da shugaban mahaddata, kuma ɗaya daga cikin fitattun marawaita Hadisi a wajen magabata na ƙwarai, marubucin littafin Al-Musannaf da Al-Musnad da Tafsiri.
HAIHUWARSA DA NEMAN ILIMINSA
An haifi Ibn Abu Shaibah a birnin Kufah dake ƙasar Iraƙi shekara ta ɗari da hamsin da tara 159 bayan hijirah, ya taso a cikin birnin Kufah kuma ya nemi ilimi a cikinta.
Ya kasance ya rayu a gidan ilimi tare da ’yan uwansa, su Al-Hafiz Usman ɗan Abu Shaibah da Al-ƙasim ɗan Abu Shaibah, bisa neman ilimin Hadisi da riwayarsa.
Mahaifinsa Al-Hafiz Ibrahim ɗan Abubakar da ɗan-ɗan uwansa Al-Hafiz Abu Jafar Muhammad ɗan Usman shahararru ne, amma Ibn Abi Shaibah shi ne mafi shahara a cikin iyalan wannan gida kuma mafi yalwar ilimi a cikinsu. Ya kasance ana buga misali da shi wajen hadda da yalwarta. Amma dangane da tafiye-tafiyensa na neman ilimi an samu cewa; ya ratsa birane da ƙauyuka wajen neman ilimi, amma tafiya mafi shahara a cikinsu su ne: Makka da Madina da Basra da Bagadaza.
ƘARNI KO ZAMANIN DA YA RAYU
Ibn Abi Shaibah ya rayu ne a tsakiyar ƙarni na biyu zuwa na uku wato a lokacin daular Abbasiyya ta farko, kuma ya riski wasu daga cikin Khalifofin wannan daula irin su: Arrashid da Al-Amin da Al-Ma'amun da Al-Mu'utasim da Al-Wasik da kuma farkon zamanin Al-Mutawakkil, domin har ma shi Al-Mutakkil ya kasance yana jawo shi jiki cikin malaman wannan daula.
A shekara ta 234 da hijirah Al-Mutawakkil ya zaɓe shi ya wakilta shi kan mayar da martani ga Mu'utazilawa bisa ƙuduri da iƙrarinsu na cewa: Al-Ƙur'ani halitta ne ba zance ne na Allah ba.
Sai Ibn Abi Shaibah ya zauna a masallacin Arrasafa dake Bagadaza, ya ragargaji hujjojinsu ya ƙarar da tanadinsu, a wannan lokacin kuwa an sami masu halarta sun kai kimanin dubu talatin (30,000), kamar yadda Imamul Bukhari ya ambata a littafinsa (Attarikh Assagir Juzu'i na 10 shafi na 335) wanda tabbas hakan ya nuna ilimin da shi Ibn Abi Shaibah yake da shi da kuma fito da ƙima da martabarsa wajen mutane ta yadda ake samun irin wannan adadi na jama'a dake halartar wurin karatunsa a lokaci guda, Imamul Bukhari ya siffanta shi cikin littafinsa (Attarikh Assagir Juzu'i na 2 shafi na 490) da cewa: tsara (sa'a) ne ga su Imamu Ahmad ɗan Hambal da Ishaq ɗan Rahawaihib da Yahaya ɗan Mu'in da Aliyu ɗan Madini.
Shi kuma Imamu Azzahabi a cikin littafinsa (Siyar A'alamu Annubala'a Juzu'i na 11 shafi na 124) ya ce: ai tsaran waɗanda aka ambata ɗin nan ne ta fuskar haihuwa da shekaru da hadda.
MALAMANSA
Ibn Abi Shaibah ya yi karatu a wajen malamai da dama, kaɗan daga cikin mafiya shahara a cikinsu sun haɗa da Sharif ɗan Abdullahi Al-ƙali da Abdullahi ɗan Mubarak da Waki'i ɗan Jirah da Usman ɗan Abi Shaibah, ɗan uwa a gare shi da Ibrahim ɗan Saduk Al-Basari da Ibrahim ɗan Mahdi da Bukar ɗan AbdulRahman Al-Kufi Al-ƙali da Junaid ɗan Abdullahi Hajjam da Hatim ɗan Wardan da sauransu, kamar yadda AlKhaɗib Al-Bagdadi ya kawo a cikin (Tarikh Bagadad Juzu'i na 10 shafi na 66)
ALMAJIRANSA
Khaɗib Al-Bagdadi ya ƙara kawo mafiya shahara cikin ɗalibansa su ne: (Imamul Bukhari da Imamu Muslim da Abu Dawud da Ibn Majah da Imam Ahmad da ɗansa Abdullahi da Imam Ibrahim Al-Harbi da Abubakar ɗan Abi Asim da Bari ɗan Mukallad da Muhammad ɗan Waddah da Abu Hatim dadai sauransu waɗanda suka rawaito Hadisi daga wurinsa lokacin da ya zo Bagdad, an lissafa kusan mutum dubu uku(3,000), waɗanda suna daga cikin waɗanda suka fi shahara
WAƊANDA SUKA FITAR DA HADISANSA
Daga cikin waɗanda suka fitar da Hadisansa akwai, dukkanin jama'a ban da Imamul Tirmizi, amma kuma Imamul Bukhari da Muslim da Abu Dawud da Ibn Majah, dukka waɗannan sun karɓo daga gare shi gaba da gaba, babu tsani.
Amma Imam Annasa'i ya karɓa a wurinsa amma da tsani a tsakaninsu. Wanda ya fi yawan fitar da Hadisan Ibn Abi Shaibah cikin almajiransa shi ne; Imam Muslim a cikin Sahihinsa, babu wanda ya rawaito adadin da ya rawaita,
domin ya rawaici hadisai kimanin dubu da ɗari biyar da arba'in (1,540), shi kuma Imamul Bukhari ya rawaici guda talatin (30).
LITTATTAFAN DA IMAM IBN ABI SHAIBAH YA WALLAFA
Malamai sun tabbatar da rubuce-rubucen Ibn Abi Shaibah, daga cikinsu akwai:- Tafsirin Al-Ƙur'ani mai girma da Littafin Al-Musannaf da Littafin Al-Musnad.
RASUWARSA
Ibn Abi Shaibah ya rasu a birnin Kufah ranar Alhamis tara ga watan Al-Muharram a shekara ta ɗari biyu da talatin da biyar 235 bayan hijira.
Full-Text Access Notice
In accordance with the NERD Policy on promoting peer-reviewed publication, public access to the full text of a project, thesis or dissertation is restricted for three years, allowing the author and supervisors sufficient time to pursue peer-reviewed publication.
During this period, researchers with legitimate academic or research purposes may request authorisation directly from the author to enable NERD to release the indexed full texts of the work using the form below.