FASSARAR WASU HADISAI DAGA CIKIN LITTAFIN MUSANNAF IBNU ABI SHAIBAH NA (ABUBAKAR BN ABI SHAIBAH) ZUWA HARSHEN HAUSA

Student: Lukman Yusuf
Supervisor: Prof Sani Yafi Musa
HOD: Dr Salim Madabo Saminu
Department of Islamic Studies
Arts
Bayero University, Kano, Kano State

Abstract

MUHIMMANCIN AIKI Haƙiƙa wannan aiki na fassara wani sashi daga Hadisan Annabi (S.A.W) da tantance su da yi musu aiki na nemo matsayinsu da wanda suka fitar dasu a cikin littattafansu (Takriji), da yin bayani akan abubuwan da suke koyarwa tare yi musu sharhi, da kuma Ta’aliqi na wasu Mas’aloli masu Muhimmanci ko rikitar wa, Saboda haka Haƙiƙa wannan aiki ya keɓanta da matsayi me girman gaske kuma me girman lada duba da matuƙar mahimmancin hadisan Annabi Alaihis-salam da koyar dasu kamar yadda Annabi S.A.W ya yi Addu’a ta Hasken Fuska da xanyantakar Ni’ima da Rahma ga dukkanin wanda Yaji wani Zance nasa kuma ya isar da shi kamar yadda yaji shi, hakanan kamar yadda ya faxa a cikin Hadisin Abdullahi bn Amr wanda Imam Al-Bukhari ya fitar : “Ku bawa Mutane Labarin duk abinda yazo daga gare ni ko da Aya ce” wanda ya shafi Alqur’ani da Hadisi domin Hadisi ma Hukuncin Ayar Alqur’ani ake ba shi domin Wahayine shima daga Allah, kuma Allah ta’ala yayi Umarni da ayi riqo da dukkanin abinda Manzo ya zo da shi alaihis-salam, acikin Suratul Hashr aya ta 7, musamman ma ga wayanda suke hausawa domin fassara Hadisai irin wayannan zai taimaka wajen fahimtar Hadisan Manzon Allah (S.A.W) a cikin sauƙi saboda kasancewar mafi yawan hausawa basa iya karatun larabci shi yasa wanna Ja’mi’ah mai albarka tayi wannan ƙokari wajen ganin an fassara littafan Addinin musulunci izuwa yaren Hausa domin yaɗa ilimi a tsakanin Al'umma musamman ma hausawa da masu jin harshen Hausa a faɗin duniya, domin wannan wani vangare ne na Da’awah da Isar da Saqon Allah. Kuma Haƙiƙa muhimmancin wannan aiki yana bayyana ne duba da matsayin hadisan Manzon Allah (S.A.W) da karantar dasu da koyar dasu, aiki ne mai matuƙar muhimmanci da tarin lada, saboda hadisin Annabi (S.A.W) shine ginshiƙin shari’ar musulunci na biyu bayan Alƙur’ani me girma. Kuma Hadisan Manzon Allah (S.A.W) sun ƙunshi: Zantukansa da kuma aiyukansa da kuma abubuwan da ya tabbatar (Abinda aka aikata a gabansa bai hana ba) da kuma halayensa da siffarsa. Haƙiƙa Ubangiji (S.W.A) aiko Manzonsa (S.A.W) ga dukkan halittu mutane da aljanu don ya shiryar dasu kamar yadda Ubangiji (S.W.A) yake cewa: “Shine wanda ya aiko muku da manzo da shiriya da addini na gaskiya don ya…” Saboda haka wajibi ne bin Sunnar Annabi (S.A.W) da yi masa biyayya kamar yadda Ubangiji (S.W.A) yake cewa: x “ya ku wayanda kuka yi imani ku bi Allah da manzonsa” Saboda haka haƙiƙa idan aka ci gaba da irin wannan aiki na fassara hadisan Annabi da yaren hausa hakan zai taimaka wajen sauƙaƙewa Al'ummar musulmi hausawa da masu jin harshen Hausa wajen fahimtar hadisan Annabi kuma hakan zai sa Addininmu ya ƙara ɗaukaka, kuma mu dawo da ƙimar harshenmu ta yadda Sauƙaƙe mana sanin Addininmu kuma wasu abubuwan baza su shige mana duhu ba domin an fito dasu fili ta yadda mutane zasu fahimta da yarensu musamman masu rauni, kuma haka zai sa rayuwarmu ta gyaru mu kyautata mu'amalolinmu na yau da kullum kuma muyi rayuwa me inganci.

Full-Text Access Notice

In accordance with the NERD Policy on promoting peer-reviewed publication, public access to the full text of a project, thesis or dissertation is restricted for three years, allowing the author and supervisors sufficient time to pursue peer-reviewed publication. During this period, researchers with legitimate academic or research purposes may request authorisation directly from the author to enable NERD to release the indexed full texts of the work using the form below.

Request authorisation from the author