FASSARAR WASU HADISAI DAGA CIKIN LITTAFIN MUSNAD IBN ABU SHAIBA NA (ABUBAKAR BN ABI SHAIBA) ZUWA HARSHEN HAUSA DAGA HADISI MAI LAMBA (28132) ZUWA (28233)
Abstract
SALON GUDANAR DA AIKI
Domin saukakawa mai karatu naga ya dace nayi bayanin salon aikina kamar
haka:
1. Ina fara rubuta Hadissan da larabci kamar yadda suka zo da cikkakken
Isnadi.
2. Ina fara fassara daga Sahabi ko Tabi’i ko wanda ma’anar Hadisin ta fara
daga kansa.
3. Ina fassara hadisin fassara mai yanci mai ma’ana.
4. Ina fadar hukuncin hadisin, idan Sahih ne ina dogara da wanda ya yi
ta’kikin littafin. kuma in yana da rauni ina fadar dalilin rauninsa. Sannan
na kawo masana hadisin da suka bayyana raunin wanda da suke rawaito
hadisin.
5. Ina takaita wadanda suka fitar da hadisan ga malamai gwargwadon abin
da ya sauwaka.
6. Nayi ta’aliki a wani bangare na hadisan wandanda nake ganin suna da
bukatan ta’aaliki. Zan kawo littafin da na dogara da su a rubuta ta’alikin.
7. Ibn Abi Shaibah yana cikin magabatan Malamai da suka rawaito hadisai,
wannan yasa ba kowane hadisin da ya rawaito ba ne za a same shi a cikin
littafan hadisan da suka zo a bayarsa, musamman hadisan da suka shafi
maganganun Sahabbai da Tabi,ai
Full-Text Access Notice
In accordance with the NERD Policy on promoting peer-reviewed publication, public access to the full text of a project, thesis or dissertation is restricted for three years, allowing the author and supervisors sufficient time to pursue peer-reviewed publication.
During this period, researchers with legitimate academic or research purposes may request authorisation directly from the author to enable NERD to release the indexed full texts of the work using the form below.