NAZARIN JIGO DA ZUBI DA TSARI A LITTAFIN KISHI KO ƁATA NA ZAHRA’U IBRAHIM WAYA...

Student: Amina Zakariyya Umar
Supervisor: Dr Ali Umar Muhammad
HOD: Dr Sani Muhammad Abdullahi
Department of Nigerian Languages
Art and Humanities
Northwest University, Kano, Kano State

Abstract

Rubutaccen wasan kwaikwayo hanya ce da marubuta kan bi domin ganin sun isar da saƙon su ga al’umma. Marubuta ƙagaggen wasan kwaikwayo kan yi amfani da hikimarsu tare da baje-kolin tunaninsu domin ganin sun fito da wasu batutuwa da suka shafi al’umma. Rubutun wasan kwaikwayo yana ɗaya daga cikin nau’ikan rubutun adabi na Hausa, sai dai ya sha bam-ban da rubutun ƙagaggen labari da waƙa, shi ya sa hanyoyin nazarinsu akwai ɗan bambanci kaɗan. Rubutaccen wasan kwaikwayo, labari ne da marubuta ke shiryawa cikin fitowa-fitowa ko shiga-shiga mai ban sha’awa da koya dabarun zaman duniya da nishaɗantarwa cikin hikima da basira. Masana Adabin Hausa da dama sun bayar da ma’anar rubutaccen wasan kwaikwayo kamar haka: Ɗangambo (1984) ya ce ‘wasa ne da ake gina shi domin kwakwayon wani labarai ko wata matsala ta rayuwa da ake son nusarwa ga jama’a cikin siffar yaƙini ko kuma rubuta shi.’’ Yahaya (1978) ya bayya wasan kwikwayo da cewa; ‘‘wasan kwaikwayo na nuni ne da aikata wani abu musamman a dandali domin ya sa nishaɗi ga masu kallo ko ya raunana musu zuciya’’ Chinwieze (1976) ya ce; ‘‘wasan kwaikwayo wani ɓangare ne da ake samar da aikin shaƙatawa ta yin sojan gona kamar kamanci a aikace ko a maganance ko a rubuce kuma a wasance.’’ Don haka wannan babi ya ƙunshi gabatarwa ne na wannan bincike da za yi a kan littafin Kishi ko Ɓata na Malama Zahra’u Ibrahim Waya. A cikin wannan babin za a kawo manufar bincike, muradin bincike, tambayoyin bincike, iyakar bincike, farfajiyar bincike da sauransu.

Full-Text Access Notice

In accordance with the NERD Policy on promoting peer-reviewed publication, public access to the full text of a project, thesis or dissertation is restricted for three years, allowing the author and supervisors sufficient time to pursue peer-reviewed publication. During this period, researchers with legitimate academic or research purposes may request authorisation directly from the author to enable NERD to release the indexed full texts of the work using the form below.

Request authorisation from the author