NAZARI A KAN KURAKURAN RUBUTUN HAUSA A JIKIN RUBUCE-RUBUCEN ABUBUWAN HAWA A BIRNIN KANO
Abstract
Tsakure
Wannan bincike mai takenn “Nazari a Kan Kurakuran Rubutun Hausa a Abubuwan Hawa a Cikin Birnin Kano” ya nazarci wasu kurakuran rubutu da aka same su a jikin abubuwan hawa a cikin birnin Kano. Binciken ya duba rubuce-rubucen da ke jikin abubuwan hawa ne kawai, inda aka fito da kurakuran rubutun aka kuma gyara su yadda suke a cikin tsarin nahawun Hausa. Wannan nazari ya yi amfani da Ra’in fiɗar kurakurai (Error Analysis Theory) na Corder (1974). Binciken ya gano akwai kurakurai da dama a cikin rubutun da ake yi a jikin abubuwan hawa, an gano akwai kurakuran haɗewa ko rabawa, misali (Allahyatsare) da kurakuran amfani da baqaqe masu lanqwasa, misali (Kudi) da kurakuran amfani da karan-ɗori, misali (Allah-yatsare) da kurakuran amfani da alamomin rubutu, misali (kum, bi, izinillah) da sauransu.
A qarshe, mai bincike ya ba da shawarar yadda masu yin rubutu da hukumomi da masu abubuwan hawa ya kamata su yi domin inganta rubutun harshen Hausa, wanda zai yi daidai da ƙa’idoijin nahawunta.
Full-Text Access Notice
In accordance with the NERD Policy on promoting peer-reviewed publication, public access to the full text of a project, thesis or dissertation is restricted for three years, allowing the author and supervisors sufficient time to pursue peer-reviewed publication.
During this period, researchers with legitimate academic or research purposes may request authorisation directly from the author to enable NERD to release the indexed full texts of the work using the form below.